Irmiya 34:11-16
11
Amma daga baya suka canja ra’ayoyinsu suka maido bayinsu suka kuma sāke bautar da su.
12
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
13
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa na yi alkawari da kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ce,
14
‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă ’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi ’yantacce.’ Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba.
15
Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar ’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana.
16
Amma yanzu kun juya kun kuma ɓata sunana; kowannenku ya mayar da bayi maza da matan da kuka ’yantar su tafi inda suka ga dama. Kun sāke tilasta su su zama bayinku.
Settings