Irmiya 3:19-25
19
“Ni kaina na faɗa, “ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza in ba ki ƙasa mai daɗi, gādo mafi kyau da wata al’umma.’ Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’ ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.
20
Amma kamar mace marar aminci ga mijinta, haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji.
21
An ji kuka a filayen tuddai, kuka da roƙon mutanen Isra’ila, domin sun lalace hanyoyinsu sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.
22
“Ku komo, mutane marasa bangaskiya; zan warkar da ku daga ja da bayanku.” “I, za mu zo wurinka, gama kai ne Ubangiji Allahnmu.
23
Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai da duwatsu banza ne; tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne akwai ceton Isra’ila.
24
Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu amfanin wahalar kakanninmu garkunan tumakinsu da na awakinsu, yaransu maza da mata.
25
Bari mu kwanta mu sha kunya, bari kuma kunyarmu ta rufe mu. Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi, da mu da kakanninmu; daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.”
Settings