Irmiya 3:12-18
12
Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa, “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba, gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.
13
Ki dai yarda da laifinki kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye, kin watsar da alheranki ga baƙin alloli a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ” in ji Ubangiji.
14
“Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona.
15
Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi.
16
A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
17
A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba.
18
A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.
Settings