Irmiya 3:14-18
14
“Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona.
15
Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi.
16
A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
17
A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba.
18
A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.
Settings