Yaƙub 5:1-6
1
Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku.
2
Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku.
3
Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe.
4
Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.
5
Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka.
6
Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba.
Settings