Yaƙub 1:22-27
22
Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.
23
Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi
24
bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa.
25
Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.
26
In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.
27
Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
Settings