Ishaya 9:1-5
1
Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun.
2
Mutanen da suke tafiya cikin duhu sun ga babban haske; a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa haske ya haskaka.
3
Ka fadada al’umma ka kuma ƙara farin cikinsu; suna farin ciki a gabanka yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi, kamar yadda mutane sukan yi farin ciki sa’ad da suke raba ganima.
4
Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi, kuka ji tsoro nauyin da ya nawaita musu, sandar da yake a kafaɗunsu, sandar masu zaluncinsu.
5
Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini zai kasance an ƙone shi zai kuma zama abin hura wuta.
Settings