Skip to content
Ishaya 65:11-16

Ishaya 65:11-16

11
“Amma game da ku waɗanda kuka yashe Ubangiji kuka manta da dutsena mai tsarki kuwa, ku da kuka shimfiɗa tebur don sa’a kuka kuma cika darunan ruwan inabin da aka dama don Ƙaddara,
12
zan ƙaddara ku ga kaifin takobi, dukanku kuma za ku sunkuya wa mai yanka; gama na yi kira amma ba ku amsa ba, na yi magana amma ba ku saurara ba. Kuka aikata mugunta a gabana kuka kuma zaɓi abin da ba na jin daɗi.”
13
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Bayin za su ci, amma ku za ku ji yunwa; bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; bayina za su yi farin ciki amma ku za ku sha kunya.
14
Bayina za su rera da farin cikin zukatansu, amma ku za ku yi kuka daga wahalar zuciya ku kuma yi kururuwa da karayar zuci.
15
Za ku bar sunanku ga zaɓaɓɓuna yă zama abin la’antarwa; Ubangiji Mai Iko Duka zai kashe ku, amma ga bayina zai ba su wani suna.
16
Duk wanda zai roƙi albarka a cikin ƙasar zai yi haka da gaskiyar Allah; wanda zai yi rantsuwa a cikin ƙasar zai rantse da gaskiyar Allah. Gama za a manta da wahalolin baya a kuma ɓoye su daga idanuna.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options