Ishaya 64:9-12
9
Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji; kada ka tuna da zunubanmu har abada. Da ma ka dube mu, muna roƙonka, gama dukanmu mutanenka ne.
10
Biranenka masu tsarki sun zama hamada; har Sihiyona ma ta zama hamada; Urushalima ta zama kango.
11
Haikalinmu mai tsarki da kuma mai daraja, inda kakanninmu suka yabe ka, an ƙone da wuta, kuma dukan abubuwan da muke ƙauna sun lalace.
12
Bayan dukan wannan, ya Ubangiji, ba za ka yi wani abu ba? Za ka yi shiru ka hore mu fiye da kima?
Settings