Ishaya 54:7-10
7
“Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.
8
Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki.
9
“A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu, sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba. Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba, ba zan ƙara tsawata miki kuma ba.
10
Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.
Settings