Ishaya 52:1-6
1
Ki farka, ki farka, ya Sihiyona, ki sanya wa kanki ƙarfi. Ki sa rigarki na daraja, Ya Urushalima, birni mai tsarki. Marasa kaciya da maƙazanta ba za su shi cikinki ba.
2
Ki kakkaɓe ƙurarki; ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima. Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki, Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.
3
Gama ga abin Ubangiji yana cewa, “An sayar da ke ba da kuɗi ba, kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”
4
Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna; a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su.
5
“Yanzu kuma me nake da shi a nan?” In ji Ubangiji. “Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a, Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.
6
Saboda haka mutanena za su san sunana; saboda haka a wannan rana za su san cewa ni ne wanda ya faɗa wannan. I, ni ne.”
Settings