Ishaya 51:9-23
9
Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi, Ya hannun Ubangiji; ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a zamanai na dā. Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa, wanda ya soki dodon ruwan nan?
10
Ba kai ba ne ka busar da teku, ka busar da ruwan zurfafa masu girma, wanda ya yi hanya a cikin zurfafan teku saboda fansassu su ƙetare?
11
Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.
12
“Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku. Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa, ’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,
13
har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci?
14
Ba da daɗewa za a ’yantar da ’yan kurkuku; ba za su mutu a kurkuku ba, ba kuwa za su rasa abinci ba.
15
Gama ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
16
Na sa maganata a bakinka na kuma rufe ka da inuwar hannuna, Na shimfiɗa sammai, na kafa harsashen duniya, na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ”
17
Ki farka, ki farka! Ki tashi, ya Urushalima, ke da kika sha daga hannun Ubangiji kwaf na fushinsa, ke da kika shanye har ƙasar kwaf kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.
18
Cikin dukan ’ya’yan da ta haifa; cikin dukan ’ya’yan da ta yi reno babu wani da zai kama hannunta.
19
Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki, wa zai ta’azantar da ke? Lalaci da hallaka, yunwa da takobi, wa zai ƙarfafa ki?
20
’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.
21
Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala, wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.
22
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Allahnki, wanda ya kāre mutanensa, “Duba, na ƙwace daga hannunki kwaf da ya sa ki tangaɗi; daga wannan kwaf, kwaf na fushina, ba za ki ƙara sha ba.
23
Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba, waɗanda suke ce miki, ‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’ Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa, kamar titin da ake takawa a kai.”
Settings