Skip to content
Ishaya 45:1-7

Ishaya 45:1-7

1
“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.
2
Zan sha gabanka in baje duwatsu; zan farfashe ƙofofin tagulla in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.
3
Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.
4
Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba.
5
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba,
6
saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
7
Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options