Ishaya 44:24-28
24
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,
25
wanda ya sassāke alamun annabawan ƙarya ya masu duba suka zama wawaye, wanda ya tumɓuke koyon masu hikima ya mai da shi banza,
26
wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa, “wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’ game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’
27
wanda ya ce wa zurfin ruwaye, ‘Ku bushe, zan kuma busar da rafuffukanku,’
28
wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’
Settings