Skip to content
Ishaya 36:1-3

Ishaya 36:1-3

1
A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin Sarki Hezekiya, Sennakerib sarkin Assuriya ya kai wa dukan birane masu kagaran Yahuda yaƙi ya kuma kame su.
2
Sai sarkin Assuriya ya aiki sarkin yaƙinsa tare da mayaƙa masu yawa daga Lakish zuwa wurin Sarki Hezekiya a Urushalima. Sa’ad da sarkin yaƙi ya tsaya a wuriyar Tafkin Tudu, a hanya zuwa Filin Mai Wanki,
3
Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka fita zuwa wurinsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options