Ishaya 33:18
Ana nuna aya 18 tare da mahallin da ke kewaye.
15
Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,
16
shi ne mutumin da zai zauna a bisa, wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse. Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.
17
Idanunku za su ga sarki a cikin kyansa ku kuma hangi ƙasar da take shimfiɗe can da nisa.
18
Cikin tunaninku za ku yi tunani firgitar da ta faru tun dā kuna cewa, “Ina hafsan nan? Ina wannan wanda yake karɓar haraji? Ina hafsan da yake lura da hasumiyoyi?”
19
Ba za ku ƙara ganin waɗannan mutane masu girman kai kuma ba, waɗannan mutane masu magana da harshen da ba ku fahimta ba.
20
Ku duba Sihiyona, birnin shagulgulanmu; idanunku za su ga Urushalima, mazauni mai lafiya, tentin da ba za a taɓa gusar ba; wanda ba a taɓa tumɓuke turakunsa ba, ko a tsinke igiyoyinta.
21
A can Ubangiji zai zama Mai Iko Duka namu. Zai zama kamar inda manyan koguna da rafuffuka suke. Matuƙan jirgin ruwa ba za su kai wurinsu ba, manyan jiragen ruwa ba za su yi zirga-zirga a kansu ba.
Settings