Ishaya 3:1-12
1
Yanzu ka duba fa, Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako daga Urushalima da Yahuda dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa,
2
jarumi, da soja, alƙali da annabi masu duba da dattijo,
3
shugaban sojojin hamsin da mutum mai makami, mai ba da shawara, gwanin sarrafa abubuwa da mai gwanintan dabo.
4
“Zan sa ’yan yara su zama shugabanninsu; ’yan yara kurum za su yi mulkinsu.”
5
Mutane za su zalunci juna mutum da mutum, maƙwabci da maƙwabci. Yara za su rena tsofaffi, ƙasƙantacce zai rena mai daraja.
6
Mutum zai kama ɗaya daga cikin ’yan’uwansa a gidan mahaifinsa ya ce, “Kana da abin sawa, ka zama shugabanmu; wannan kango kuma yă zama a ƙarƙashinka!”
7
Amma a ranan nan zai tā da murya ya ce, “Ba ni ba dai. Ba ni da abinci ko abin sawa a gidana; kada ka mai da ni shugaban mutane.”
8
Urushalima tana tangaɗi, Yahuda yana fāɗuwa; maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji, suna rena ɗaukakar kasancewarsa.
9
Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa.
10
Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau, gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi.
11
Kaiton masu mugunta! Masifa tana a kansu! Za a rama abin da hannuwansu suka yi.
12
Matasa suna zalunta mutanena, mata suna mulki a bisansu. Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku; suna karkatar da ku daga hanya.
Settings