Ishaya 17:7-11
7
A wannan rana mutane za su nemi Mahaliccinsu su kuma juye idanunsu ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
8
Ba za su dubi bagade ba, waɗanda suke aikin hannuwansu, ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi.
9
A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango.
10
Kun manta da Allah Mai Cetonku; ba ku tuna da Dutse, kagararku ba. Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,
11
ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma, da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure, duk da haka girbin ba zai zama kome ba a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.
Settings