Skip to content
Ishaya 17:1-6

Ishaya 17:1-6

1
Abin da Allah ya faɗa game da Damaskus. “Duba, Damaskus ba za tă ƙara zama birni ba amma za tă zama tsibin juji.
2
Za a watse a bar biranen Arower a bar wa tumaki da shanu, waɗanda za su kwanta, ba tare da wani wanda zai tsorata su ba.
3
Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim, ikon sarauta kuma daga Damaskus; raguwar Aram za tă zama kamar darajar Isra’ila,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
4
“A wannan rana ɗaukakar Yaƙub za tă ƙare; kitsen jikinsa zai lalace.
5
Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye ya kuma girbe hatsin da hannunsa kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi a Kwarin Refayim.
6
Duk da haka waɗansu kala za su ragu, sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun, aka bar ’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai ’ya’ya,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options