Hosiya 4:1-6
1
Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa, gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar. “Babu aminci, babu ƙauna, babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
2
Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa, yin sata da zina; sun wuce gona da iri, kisankai a kan kisankai.
3
Saboda wannan ƙasar tana makoki, kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace; namun jeji da tsuntsayen sararin sama da kuma kifin teku suna mutuwa.
4
“Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma, kada wani mutum yă zargi wani, gama mutanenka suna kama da waɗanda suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne.
5
Kuna tuntuɓe dare da rana, annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku. Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku,
6
mutanena suna hallaka saboda jahilci. “Domin kun ƙi neman sani, ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina; domin kun ƙyale dokar Allahnku, ni ma zan ƙyale ’ya’yanku.
Settings