Hosiya 2:8-13
8
Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.
9
“Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna, da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa. Zan karɓe ulu nawa da lilina, da take niyya ta rufe tsiraicinta.
10
Saboda haka yanzu zan buɗe tsiraicinta a idanun kwartayenta; ba wani da zai ƙwace ta daga hannuwana.
11
Zan tsayar da dukan bukukkuwarta, bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata, kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta.
12
Zan lalatar da inabinta da kuma itatuwan ɓaurenta, waɗanda take cewa su ne abin da kwartayenta suka biya; zan mayar da su kurmi, namun jeji kuwa za su ci su.
13
Zan hukunta ta saboda kwanakin da ta ƙone turare wa Ba’al; ta yi wa kanta ado da zobai da duwatsu masu daraja, ta bi kwartayenta, amma ta manta da ni,” in ji Ubangiji.
Settings