Hosiya 2:1
Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
“Ka ce da ’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da ’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’
2
“Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata, gama ita ba matata ba ce, ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta tă daina karuwancinta da kuma rashin aminci a tsakanin nononta.
3
In ba haka ba zai tuɓe ta tsirara in bar ta kamar yadda take a ranar da aka haife ta; zan sa ta zama kamar hamada, in mayar da ita busasshiyar ƙasar, in kashe ta da ƙishirwa.
4
Ba zan nuna wa ’ya’yanta ƙaunata ba, domin su ’ya’yan zina ne.
Settings