Skip to content
Hosiya 13:15

Hosiya 13:15

Ana nuna aya 15 tare da mahallin da ke kewaye.
12
An yi ajiyar laifin Efraim, aka lissafta zunubansa.
13
Naƙuda ta zo masa kamar a mace mai haihuwa, amma shi yaro ne marar hikima; sa’ad da lokaci ya kai, ba ya zuwa inda mahaifa ta buɗe.
14
“Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba,
15
ko da ma ya ci gaba cikin ’yan’uwansa. Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo, tana hurawa daga hamada; maɓulɓularsa za tă kafe rijiyarsa kuma ta bushe. Za a kwashi kaya masu daraja na ɗakin ajiyarsa ganima.
16
Dole mutanen Samariya su ɗauki laifinsu, domin sun tayar wa Allahnsu. Za a kashe su da takobi; za a fyaɗa ƙananansu da ƙasa, za a ɓarke matansu masu ciki.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options