Ibraniyawa 5:11-14
11
Muna da abubuwa masu yawa da za mu faɗa game da wannan batu, sai dai yana da wuya a bayyana, da yake ba ku da saurin ganewa.
12
Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yă sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai kauri ba!
13
Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar jariri ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba.
14
Amma abinci mai kauri na balagaggu ne, waɗanda suka hori kansu don su bambanta tsakanin nagarta da mugunta.
Settings