Skip to content
Ibraniyawa 4:1-7

Ibraniyawa 4:1-7

1
Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga.
2
Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba.
3
Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya.
4
Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.”
5
Haka kuma a nassin nan ya ce, “Ba za su taɓa shiga hutuna ba.”
6
Har yanzu dai da sauran dama domin waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya.
7
Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options