Ibraniyawa 3:1-10
1
Saboda haka, ’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa.
2
Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah.
3
An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.
4
Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.
5
Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.
6
Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.
7
Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,
8
kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada,
9
inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.
10
Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’
Settings