Skip to content
Farawa 6:5-12

Farawa 6:5-12

5
Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.
6
Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.
7
Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
8
Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
9
Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.
10
Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
11
Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.
12
Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options