Farawa 3:1-15
1
To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
2
Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun,
3
amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
4
Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba.
5
Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
6
Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.
7
Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.
8
Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.
9
Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
10
Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
11
Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
12
Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
13
Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
14
Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.
15
Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
Settings