Skip to content
Farawa 28:6-9

Farawa 28:6-9

6
Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,”
7
ya kuma san cewa Yaƙub ya yi biyayya da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, ya kuwa tafi Faddan Aram.
8
Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba;
9
saboda haka sai ya tafi wurin Ishmayel ya auri Mahalat, ’yar’uwar Nebayiwot da kuma ’yar Ishmayel ɗan Ibrahim, ban da matan da yake da su.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options