Farawa 15:7-11
7
Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.”
8
Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?”
9
Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.”
10
Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.
11
Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su.
Settings