Skip to content
Farawa 11:1-9

Farawa 11:1-9

1
To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
2
Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.
3
Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.
4
Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”
5
Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.
6
Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.
7
Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”
8
Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.
9
Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options