Galatiyawa 6:1-5
1
’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.
2
Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
3
In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi.
4
Kowa yă auna ayyukansa. A sa’an nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba,
5
gama kowa zai ɗauki kayansa.
Settings