Ezra 8:27-32
27
kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya.
28
Na ce masa, “Ku da kayan nan tsarkaka ne ga Ubangiji. Azurfa da zinariya ɗin, bayarwa ce ta yardar rai ga Ubangiji, Allah na kakanninku.
29
Ku lura da su da kyau har sai kun isa Urushalima. Ku auna su a shirayin haikalin Ubangiji a Urushalima, a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai na Isra’ila.”
30
Sa’an nan sai firistoci, da Lawiyawa suka karɓi azurfa da zinariya da kuma tsarkakan kwanonin da aka auna don a kai haikalin Allahnmu a Urushalima.
31
A rana ta goma sha biyu ga watan farko, muka tashi daga bakin rafin Ahawa don mu tafi Urushalima. Alherin Allahnmu yana tare da mu, ya kuma kāre mu daga magabta da ’yan fashi.
32
Muka iso Urushalima, inda muka huta kwana uku.
Settings