Skip to content
Ezra 8:24-29

Ezra 8:24-29

24
Sai na keɓe manyan firistoci guda goma sha biyu tare da Sherebiya, Hashabiya da kuma ’yan’uwansu guda goma.
25
Na auna musu zinariya da azurfa, da kwanoni waɗanda sarki da mashawartansa, da sauran abokan aikinsa, da Isra’ilawan da suke can suka bayar domin haikalin Allahnmu.
26
Na auna musu talenti 650 na azurfa, talenti ɗari na kwanonin azurfa, talenti 100 na zinariya,
27
kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya.
28
Na ce masa, “Ku da kayan nan tsarkaka ne ga Ubangiji. Azurfa da zinariya ɗin, bayarwa ce ta yardar rai ga Ubangiji, Allah na kakanninku.
29
Ku lura da su da kyau har sai kun isa Urushalima. Ku auna su a shirayin haikalin Ubangiji a Urushalima, a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai na Isra’ila.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options