Ezra 7:23-28
23
A yi duk abin da Allah na sama ya ce don haikalin Allah na sama, sai a yi shi da himma. Me zai sa a jawo wa sarki da ’ya’yansa fushin Allah?
24
Ku kuma san cewa, ba ku da ikon sa firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofin haikali, da masu aiki a gidan Allah, ko waɗansu masu aiki a haikali su biya haraji, ko kuɗin shiga.
25
Kai kuma Ezra, bisa ga hikimar da Allah ya ba ka, sai ka zaɓi mahukunta da alƙalai waɗanda za su zama masu yanke hukunci ga dukan mutanen Kewayen Kogin Yuferites, duk waɗanda suka san dokokin Allahnka, ka kuma koya wa duk waɗanda ba su san dokokin ba.
26
Ba shakka duk wanda bai yi biyayya da dokokin Allahnka ba, da kuma dokokin sarki ba dole a yanke masa hukuncin kisa, ko hukuncin kora, ko hukuncin raba shi da mallakarsa, ko kuma hukuncin kulle shi a kurkuku.
27
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na kakanninmu, ya taɓa zuciyar sarki don yă kawo ɗaukaka ga haikalin Allah a Urushalima ta wannan hanya.
28
Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a gaban sarki da mashawartansa, da kuma duk manyan masu muƙami nasa. Gama Ubangiji Allahna yana tare da ni, sai na sami ƙarfin hali na tattara shugabannin mutane daga Isra’ila, don mu tafi tare.
Settings