Skip to content
Ezra 7:14-21

Ezra 7:14-21

14
Sarki ne da mashawartansa guda bakwai suka aike ka don ka je ka ga halin da Yahuda da Urushalima suke ciki game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka.
15
Za ka kuma tafi da zinariya da azurfa waɗanda sarki da mashawartansa suka ba da kyautar yardar rai ga Allah na Isra’ila, wanda haikalinsa ke a Urushalima,
16
haɗe da duk zinariya da azurfan da za ka iya samu a Babilon, da kuma duk bayarwar yardar rai daga mutane da firistoci, domin haikalin Allahnsu da yake a Urushalima.
17
Ka tabbata ka yi amfani da kuɗin nan don ka sayi bijimai, da raguna, da ’yan raguna, da hadayu na gari, da na sha, ka kuma miƙa su a kan bagade na haikalin Allahnka a Urushalima.
18
Sa’an nan kai da ’yan’uwanka Yahudawa ku yi abin da kuka ga ya fi kyau da sauran zinariya da azurfa ɗin bisa ga nufin Allah.
19
Ka kai wa Allah na Urushalima duk kayan da aka ba ka amanarsu don yin sujada a haikalin Allahnka.
20
Duk kuma wani abin da ake bukata domin haikalin Allahnka, daga ɗakunan ajiya sarki za ka fitar da kuɗin.
21
Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci,
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options