Ezra 4:7-16
7
A zamanin Artazerzes sarkin Farisa kuma, sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da sauran abokansu suka rubuta wasiƙa zuwa ga Artazerzes. Aka rubuta wasiƙar da harufan Arameyik, aka kuma fassara ta a yaren Arameyik.
8
Rehum shugaban rundunar soja, da Shimshai marubuci, suka rubuta wasiƙar a kan Urushalima zuwa ga sarki Artazerzes, suka ce.
9
Rehum shugaban sojoji, da Shimshai marubuci, da sauran abokansu, wato, alƙalai, da masu riƙe da muƙamai daga Farisa, Uruk da Babilon, mutanen Elam da na Shusha,
10
da sauran mutane waɗanda mai girma Osnaffar ya kwaso, ya zaunar da su cikin birnin Samariya da sauran wurare na Kewayen Kogin Yuferites.
11
(Ga abin da suka rubuta.) Zuwa ga sarki Artazerzes. Daga bayinka, mutanen Kewayen Kogin Yuferites.
12
Ya kamata sarki ya san cewa Yahudawan da suka hauro wurinmu daga wurinka, sun je Urushalima suna sāke gina wannan mugun birni mai tawaye. Suna sāke gyara katangar, suna kuma gyara harsashin katangar.
13
Ya kamata fa, sarki ya san cewa in aka sāke gina wannan birni duk da katangar birnin, mutanen birnin ba za su dinga biyan haraji, da kuɗin shiga, da na fitar da kaya ba, wannan zai sa aljihun masarauta yă bushe.
14
Tun da yake muna ƙarƙashin fada, bai kyautu mu bari a rena sarki ba, Saboda haka muke sanar da sarki,
15
domin a bincika a littattafan tarihin kakanninka. Za ka ga cewa wannan birni mai tawaye ne. Tun daga zamanin dā wannan birnin yana ba sarakuna da yankuna damuwa. Wannan ne ya sa aka ragargazar da birnin.
16
Muna sanar da sarki cewa in har aka sāke gina wannan birnin da katangarsa, zai zama ka rasa kome a gefen Kewayen Kogin Yuferites ke nan.
Settings