Ezra 10:2-12
2
Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam ya ce wa Ezra, “Mun yi wa Allah rashin aminci ta wurin yin auratayya da maƙwabtanmu, amma duk da haka bai yashe mutanen Isra’ila ba.
3
Yanzu bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori matan da yaransu bisa ga abin da ranka yă daɗe da sauran shugabannin da kuke girmama umarnin Allah kuka shawarce mu, bari mu yi haka bisa ga doka.
4
Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, za mu ba ka goyon baya. Saboda haka ka yi ƙarfin hali ka aikata shi.”
5
Sai Ezra ya tashi ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra’ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.
6
Sa’an nan Ezra ya tashi daga gidan Allah ya tafi gidan Yehohanan ɗan Eliyashib, a can ma bai ci wani abu ba, bai sha ruwa ba domin ya ci gaba da yin baƙin cikin rashin aminci na waɗanda suka dawo daga bauta.
7
Aka yi shela a duk fāɗin Yahuda da Urushalima cewa dukan waɗanda suka dawo daga bauta su tattaru a Urushalima.
8
Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama’ar da suka dawo daga bauta. Haka shugabanni da dattawa suka zartar.
9
A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.
10
Sai Ezra firist ya miƙe tsaye ya yi musu magana ya ce, “Kun yi rashin aminci; kun aure mata baƙi, ta haka kuka ƙara kan zunubin Isra’ila.
11
Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.”
12
Mutanen kuwa suka tā da murya da ƙarfi suka ce, “Gaskiya ka faɗa, dole mu yi yadda ka ce,
Settings