Ezekiyel 8:1-8
1
A shekara ta shida, a wata shida a ranar ta biya, yayinda nake zaune a gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, hannun Ubangiji Mai Iko Duka ya zo a kaina a can.
2
Na duba, sai na ga siffa kamar na mutum. Daga kwankwaso zuwa ƙasa ya yi kamar wuta, kuma daga kwankwaso zuwa sama kamanninsa ya yi haske yana ƙyalli kamar ƙarfe mai haske.
3
Ya miƙa abin da ya yi kamar hannu ya kama a gashin kaina. Ruhu ya ɗaga ni tsakanin sama da ƙasa, a cikin wahayoyi kuma Allah ya ɗauke ni zuwa Urushalima, zuwa ƙofa zuwa gabas na cikin fili, inda gunki mai tsokanar kishi yake tsaye.
4
A can gabana kuwa ga ɗaukakar Allah na Isra’ila, kamar a wahayin da na gani a fili.
5
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, duba waje arewa.” Sai na duba, a mashigin arewa na ƙofar bagaden kuwa na ga wannan gunki na tsokanar kishi.
6
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwan banƙyamar da gidan Isra’ila ke yi a nan, abubuwan da za su kore ni daga wuri mai tsarkina? Amma za ka ga abubuwan da suka ma fi banƙyama.”
7
Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango.
8
Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.
Settings