Ezekiyel 7:23-27
23
“ ‘Ka shirya sarƙoƙi, domin ƙasar ta cika da alhakin jini, birnin kuma ya cika da rikici.
24
Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku; zan kawo ƙarshen fariyar masu ƙarfi, Wurare Masu Tsarkinsu za su ƙazantu.
25
Sa’ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.
26
Masifa a kan masifa za su zo, jita-jita kuma a kan jita-jita. Za su yi ƙoƙarin samun wahayi daga annabi; koyarwar doka ta wurin firist za tă ɓace, kamar yadda shawarar dattawa za tă ɓace.
27
Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya, hannuwan mutanen ƙasar kuma za su yi rawa. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su bisa ga ma’auninsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Settings