Ezekiyel 47:6-12
6
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan?” Sa’an nan ya komo da ni zuwa bakin kogin.
7
Sa’ad da na iso can, sai na ga itatuwa masu yawa a kowane gefen kogin.
8
Sai ya ce mini, “Wannan ruwa yana malalowa zuwa yankin gabas ya kuma gangaro zuwa cikin Araba, inda zai shiga Teku. Sa’ad da ya shiga cikin Tekun sai ruwan a can ya zama mai daɗi.
9
Tarin halittu masu rai za su rayu a duk inda ruwan ya malalo. Za a kasance da kifi masu yawa, domin wannan ruwa yana malalowa a can yana kuma mai da ruwan gishiri yă zama ruwa mai daɗi; saboda haka duk inda ruwan ya malalo, kome zai rayu.
10
Masunta za su tsaya a gaɓar; daga En Gedi zuwa En Eglayim, za a kasance da wuraren jefa abin kamun kifi. Za a sami kifayen iri-iri, kamar kifaye Bahar Rum.
11
Amma fadamun da tafkunan ba za su zama masu daɗi ba; za a bar su a gishirinsu.
12
’Ya’yan itatuwa na kowane iri za su yi girma a kowane gefen kogin. Ganyayensu ba su bushe ba, ba kuwa za su fasa yin ’ya’ya ba. Kowane wata za su ba da ’ya’ya domin ruwa daga wuri mai tsarki yana malalo musu. ’Ya’yansu za su zama abinci, ganyayensu kuma za su zama magani.”
Settings