Ezekiyel 45:1-4
1
“ ‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki.
2
Daga cikin wannan, sashe guda da yake murabba’i mai tsawo kamu 500 zai zama don wuri mai tsarki, kamu 50 kewaye da shi zai zama fili.
3
A cikin yanki mai tsarki, ka auna tsawo kamu 25,000 da kuma fāɗi kamu 10,000. A cikinsa wuri mai tsarki zai kasance, Wuri Mafi Tsarki.
4
Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki.
Settings