Ezekiyel 44:28-31
28
“ ‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu.
29
Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu.
30
Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku.
31
Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba.
Settings