Skip to content
Ezekiyel 36:8-15

Ezekiyel 36:8-15

8
“ ‘Amma ku, ya duwatsun Isra’ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanena Isra’ila, gama ba da daɗewa ba za su komo gida.
9
Na damu da ku kuma zan dube ku da tausayi; za ku nome ku kuma shuka,
10
zan kuma riɓaɓɓanya mutane a kanku, dukan gidan Isra’ila ke nan. Za a zauna a birane a kuma sāke gina rusassun wurare.
11
Zan sa mutane da dabbobi su yi yawa a kanku, za su kuma ba da ’ya’ya su kuma yi yawa. Zan zaunar da mutane a kanku kamar dā zan kuma sa ku wadaita fiye da dā. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
12
Zan sa mutanena Isra’ila su yi tafiya a kanku. Za su mallake ku, za ku kuma zama gādonsu; ba za ku ƙara sa su rasa ’ya’yansu ba.
13
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin mutane suna magana game da ku cewa, “Kun cinye mutane kuka kuma sa al’ummarku ta rasa ’ya’yanta,”
14
saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ko ku sa al’ummarku ta rasa ’ya’ya ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
15
Ba zan ƙara bari ku ji maganar banza ta al’ummai ba, ba kuwa za ku ƙara shan ba’ar mutane ko in sa al’ummarku ta fāɗi ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options