Ezekiyel 32:9-12
9
Zan dami zukatan mutane masu yawa sa’ad da na kawo maka hallaka a cikin al’ummai, a cikin ƙasashen da ba ka taɓa sani ba.
10
Zan sa mutane da yawa su giggice saboda abin da ya same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobina a gabansu. A ranar fāɗuwarka kowannensu zai yi rawar jiki a kowane lokaci saboda ransa.
11
“ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Takobin sarkin Babilon zai auko maka.
12
Zan sa jama’arka su mutu ta wurin takuban ƙarfafan mutane, masu bantsoro na dukan al’ummai. Za su lalatar da girman kan Masar, su kuma tumɓuke dukan jama’arta.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.