Skip to content
Ezekiyel 32:1-16

Ezekiyel 32:1-16

1
A shekara ta goma sha biyu, a wata na goma sha biyu a rana ta fari, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa. “ ‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai; kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna kana ɓullowa cikin rafuffukanka, kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka.
3
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Da taron jama’a masu yawa zan jefa abin kamun kifi a kanka, za su kuwa jawo ka da abin kamun kifi.
4
Zan jefar da kai a ƙasa zan jefa ka a fili. Zan sa dukan tsuntsayen sararin sama su zauna a kanka dukan namun jeji na duniya kuma za su ƙosar da kansu a kanka.
5
Zan baza namanka a kan duwatsu in kuma cika kwaruruka da gawarka.
6
Zan jiƙa ƙasar da jininka mai gudu har zuwa duwatsu, magudanan ruwa za su cika da namanka.
7
Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu; zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba.
8
Dukan haskokin sammai za su zama duhu a kanka; zan kawo duhu a kan ƙasarka, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9
Zan dami zukatan mutane masu yawa sa’ad da na kawo maka hallaka a cikin al’ummai, a cikin ƙasashen da ba ka taɓa sani ba.
10
Zan sa mutane da yawa su giggice saboda abin da ya same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobina a gabansu. A ranar fāɗuwarka kowannensu zai yi rawar jiki a kowane lokaci saboda ransa.
11
“ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Takobin sarkin Babilon zai auko maka.
12
Zan sa jama’arka su mutu ta wurin takuban ƙarfafan mutane, masu bantsoro na dukan al’ummai. Za su lalatar da girman kan Masar, su kuma tumɓuke dukan jama’arta.
13
Zan hallaka dukan dabbobinta da suke kusa da ruwaye masu yawa ƙafar mutum ba zai ƙara damunsa ko kofaton dabba ya gurɓata shi.
14
Sa’an nan zan sa ruwanta su kwanta in sa rafuffukanta su gudu kamar mai, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
15
Sa’ad da na mai da Masar kufai na kuma raba ƙasar da abin da take cike da shi, sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, a sa’an nan ne za su san cewa ni ne Ubangiji.’
16
“Wannan ne makokin da za a yi mata. ’Yan matan al’ummai za su rera shi; gama Masar da dukan jama’arta za su rera shi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options