Ezekiyel 24:20-27
20
Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa
21
faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku. ’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi.
22
Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba.
23
Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi.
24
Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’
25
“Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka ’ya’yansu maza da mata,
26
a ranan nan wanda ya tsere zai zo don yă ba ka labari.
27
A lokacin bakinka zai buɗe, za ka yi magana da shi ba kuwa za ka ƙara yin shiru ba. Ta haka za ka zama alama gare su, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.”
Settings