Skip to content
Ezekiyel 23:44-49

Ezekiyel 23:44-49

44
Suka kuwa kwana da ita. Kamar yadda maza suke kwana ta karuwa, haka suka kwana da waɗannan lalatattun mata, Ohola da Oholiba.
45
Amma masu adalci za su hukunta su irin da akan yi wa matan da suka yi zina suka kuma yi kisa, domin su mazinata ne kuma jini yana a hannuwansu.
46
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kawo taron mutane a kansu a kuma miƙa su don a firgitar da su a kuma washe su.
47
Taron mutanen za su jajjefe su, su kuma sassare su da takuba; za su kashe ’ya’yansu maza da mata su kuma ƙone gidajensu.
48
“Ta haka zan kawo ƙarshe ga lalaci a ƙasar, don dukan mata su ji gargaɗi kada kuma su kwaikwaye ku
49
Za ku sha hukuncin lalacinku ku kuma ɗauki hakkin zunuban bautar gumaka. Sa’an nan za ku san cewa Ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options