Ezekiyel 24:1-14
1
A shekara ta tara, a wata na goma, a rana ta goma, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka rubuta wannan rana, wannan rana, domin sarkin Babilon ya yi ƙawanya wa Urushalima a wannan rana.
3
Ka faɗa wa wannan gidan ’yan tawaye wani misali ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka sa tukunyar dahuwa; ka sa ta a kan wuta ka kuma zuba ruwa a cikinta.
4
Ka sa gunduwoyin nama a cikinta dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa. Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau;
5
ka kama mafi kyau daga cikin garken. Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan; ka sa ta tafasa ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta.
6
“ ‘Gama wannan shi ne abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini, ga tukunya wadda take da tsatsa, wadda tsatsarta ba za tă fita ba! Ka fitar da shi gunduwa-gunduwa ba tare da jefa ƙuri’a a kansu ba.
7
“ ‘Gama zubar da jini yana a tsakiyarta, ta zubar da shi a dutsen da yake a fili; ba tă zubar da shi a ƙasa ba, inda ƙura za tă rufe shi.
8
Don a zuga hasala a kuma yi sakayya na sa jininta a dutsen da ba a rufe ba, saboda kada a rufe.
9
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini! Ni ma zan jibge itace da yawa.
10
Ka tula gumagumai ka kuma ƙuna wuta. Ka dafa naman da kyau, kana haɗawa da yaji; ka kuma bar ƙasusuwan su ƙone.
11
Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur domin dattinta ya narke tsatsarta kuma ta ƙone.
12
Ta gajiyar da dukan ƙoƙari; ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba, kai, ko a wuta ma.
13
“ ‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.
14
“ ‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Settings