Tsallake zuwa abun ciki
Ezekiyel 20:45-49

Annabci a kan kudanci

Ezekiyel 20:45-49
45
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
46
“Ɗan mutum, ka kafa fuskarka wajen kudu; ka yi wa’azi a kan kudu ka kuma yi annabci a kan kurmin ƙasar kudu.
47
Ka faɗa wa kurmin kudanci, ‘Ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da sa maka wuta, za tă kuwa cinye dukan itatuwanki sarai, da ɗanye da busasshe. Ba za a kashe wutar da take ci ba, kuma kowace fuska a kudu zuwa arewa za tă ƙone.
48
Kowa zai san cewa Ni Ubangiji ne ya ƙuna ta; ba za a kashe ta ba.’ ”
49
Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Suna zance a kaina cewa, ‘Ba misalai kawai yake yi ba?’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options